Balagh
Aikin "Balagh" wato "isarwa" yana Magana ne akan tarjamar maanonin Alƙurani mai girma, zuwa harsuna masu yawa na ko ina a faɗin duniyar nan, kuma wannan wani ɗamba ne na ƙoƙarin isrda maganar Allah s.w.t zuwa ga dukkan talikai a duk vangarorin duniya, hakanan wannan aiki ya dogara ne akan sauti da surah.
Wannan aiki na "Balagh" ya ƙunshi hidimoni masu yawa, daga ciki akwai:
1-Yiwuwar bincika kowane hoto da ya ƙunsa kai tsaye.
2-Yiwuwar bincika kowace surah.
3-Darje naui cikin waɗanda ake dasu.
4-Zaa iya canza hasken tashar.
5-Akwai wajen tara duk abinda ya burge ka, domin sauƙin dawowa gareshi sand aka buƙaci hakan.
6- Aika duk abinda ka buƙata na bidiyo zuwa ga abokanka ta hanyar Email.
7-Tarayya da abokanka wajen zaƙulo abubuwan da suka birgeka da yaɗa shi a shafukan zumunci kamar facebook da twitter da sauransu.
Manufar wannan aiki na "Balagh":shine isarda maganar Allah s.w.t zuwa ga mutane baki ɗaya, da dukkan harsunan da suke Magana dasu, wanda zai dace da buƙatunsu , kamar yadda wannan aiki ke nufin sanya wani ɗamba na sabunta hnayar kira zuwa ga Allah domin ta dace da zamani, ta hanyar fasahar zamani.
Kamar yadda aikin ke gabtarwa makaranta Alƙurani mai girma saukarsa daga bakin ƙwararrun makaranta, waɗanda suka zarta 33, sama da bidiyo 313, da tarjamar karatun a lokaci guda zuwa ga harsuna masu yawan gaske, kamar (Ingilishi – Jamusanci – Cananci – Indonesiyanci – Bangale – Farisanci – Faransanci – Hausa - Spaniyanci – Turkiyanci) .